• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

CHARLES SOLUDO YA ZAMA GWAMNAN JIHAR ANAMBRA

ByYusuf Yau

Nov 11, 2021

Karshe dai hukumar zaben Najeriya INEC ta aiyana dan takarar jam’iyyar APGA a zaben gwamnan jihar Anambra Charles Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da a ka gudanar ranar asabar 6 ga watan nan na nuwamba.
Wannan ya biyo bayan kammala zaben a wasu mazabu a karamar hukumar Ihiala inda Soludo ya kara samun zarra a kuri’un.
Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Soludo murna da yabawa hukumar zaben kan yanda ta gudanar da zaben cikin nasara.
Zaben na daya daga zabukan da a ka samu mafi karancin masu kada kuri’a musamman don fargabar hari daga ‘yan tawayen IPOB.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *