• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BURTANIYA TA TAIMAKA TA SA BAKI KAN NNAMDI KANU-LAUYAN KANU

Lauyan shugaban ‘yan awaren Biafra Namadi Kanu ya bukaci gwamnatin Burtaniya ta sa baki wajen lamuran diflamasiyya don a sake Kanun.

Lauyan Aloy Ejimakor ya yi bukatar ce a wasika da ya aikatawa jakadiyar Burtaniya a Najeriya Catriona Laing.

Kanu dai na da shaidar dan kasa a Burtaniya baya ga Najeriya da ya son a raba don kafa kasar Biyafara.

A yanzu haka Kanu na hannun jami’an tsaron DSS don jiran shari’ar sa ranar 26 ga watan nan a kotun Jostis Binta Nyako.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *