Burtaniya ta dawo da fam miliyan 4.2 na almundahanar tsohon gwamnan Delta James Ibori ga Najeriya.
Ministan shari’a Abubakar Malami ya baiyana cewa Burtaniya ta turo kudin a canjin Naira zuwa asusun gwamnati.
Gwamnatin ta nuna kudin sun samu ne don gamsuwa da ketare su ka yi cewa Najeriya na aiki da kudin da a ka gano ta hanyar da ta dace.
A baya dai gwamnatin jihar Delta ta dau matakan mallakar kudin cewa na ta ne inda gwamnatin taraiya ke cewa za ta yi amfani da kudin ta aiyukan raya kasa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀