• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BUHARI: ‘YAN NAJERIYA NA DA HURUMIN YIN ZANGA-ZANGA KO BAIYANA RA’AYIN SU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya na da hurumin zanga-zanga ko baiyana ra’ayin su cikin yanayi na tsakanaki kamar yanda ya ke kunshe a sashe na 49 na tsarin mulkin kasar.

Shugaba Buhari ya baiyana haka ne a jawabi na farko da ya gabatar kan zanga-zangar endsars da ta sauya zuwa kashe-kashe da kone-kone. Shugaban ya ce an samu abun takaici game da zanga-zangar da a farko matasa sun yi da manufa mai kyau da ta sa tuni a soke rundunar SARS.

Shugaban ya ce an samu fyade, kashe rayukan da ba su yi wa kowa laifi ba, balle gidajen yari biyu da sake fursunoni da kona kadarori da dama. Duk da shugaban bai ambaci ganin matasan na cin abinci mai tsada da sanya kaya masu tsada da ma rike makamai.

Sannan ya yi mu su tayin da a ke yi wa talakawa na cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati na rage talauci irin N-POWER, Tredamoni, Marketmoni da sauran su.

Wannan ya kai ga shugaban ya bugi kirjin cewa ba wata gwamnati a baya da ta aiwatar da shirye-shirye na yaki da talauci kamar gwamnatin sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “BUHARI: ‘YAN NAJERIYA NA DA HURUMIN YIN ZANGA-ZANGA KO BAIYANA RA’AYIN SU”
 1. I was suggested this blog by my cousin. I am not sure whether this
  post is written by him as no one else know such detailed about my trouble.
  You’re amazing! Thanks!

 2. What’s up colleagues, how is the whole thing, and what you desire to
  say concerning this post, in my view its genuinely awesome designed for
  me.

 3. Thanks for any other excellent post. The place else could anybody get that kind of information in such a perfect manner of writing?

  I have a presentation subsequent week, and I am at
  the search for such info.

Leave a Reply

Your email address will not be published.