Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai wuce zuwa Landan a ranar Juma’a domin abin da ofishinsa ya bayyana a matsayin ganin likita.’
“Zai dawo kasar a makon na biyu na watan Yulin, 2021,” in ji hadimin shugaban kasar Femi Adesina; wanda ke nuna shugaban na Najeriya zai kwashe kimanin makonni biyu a Landan don kula da lafiyarsa, ya tabbatar da sabuwar tafiya a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Alhamis.
Idan za’a tuna Shugaban ya dawo daga tafiyarsa ta karshe daga Landan a watan Afrilu, inda yayi tafiyar a ranar 30 ga Maris kuma ya dawo kasar bayan makonni biyu.
Kafin tafiyar ta watan Afrilu, Buhari ya kuma tafi Landan don duba lafiyarsa a watan Mayun 2018.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
It’s awesome to pay a quick visit this site and reading the views of all
colleagues concerning this post, while I am also zealous of getting knowledge.