• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BUHARI KA KORI GWAMNAN BABBAN BANKI EMEFIELE – FEMI FALANA

Babban lauya a Najeriya Femi Falana ya shawarci shugaba Buhari ya kori gwamnan babban banki Godwin Emefiele daga mukamin sa.

Falana a taro da matasa a jihar Ekiti, ya ce irin karfin da gwamnan banki ke da shi, ya nuna ba daidai ba ne ya fito takarar siyasa.

Hakanan Falana ya nuna tun da Emefiele dan jam’iyyar APC ne mai rejistra, abu ne da ba za a amince da shi ba a ajiye takardun gudanar da zaben 2023 a ma’adanar babban bankin matukar Emefiele na kan kujerar.

Don haka Falana ya bukaci shugaban ya kori Emefiele daga gwamnan babban bankin don kar barin sa a kujera ya jawo matsala.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.