• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BOM YA TASHI DA WATA ‘YAR JARIDA A BIRNIN ADEN

ByNoblen

Nov 10, 2021

Bom da a ka dana a mota a birnin Aden ya yi sanadiyyar mutuwar wata ‘yar jarida da ke da juna biyu.

‘Yar jaridar mai suna Rasha Abdullah Al Harazi na tare da mijin ta a motar mai suna Mahmud Al Atmi wanda shi ma dan jarida ne.

Yayin da Rasha ta riga mu gidan gaskiya, Mahmud ya samu raunuka ne.
Duk ‘yan jaridar biyu na aiki ne da wani gidan talabijin na gabar ta tsakiya.

Gwamnatin Yaman na aiki daga birnin Aden na kudanci don yanda ‘yan tawayen HOUTHI bisa goyon bayan Iran ke mamaye da babban birnin kasar Sanaa.

A watan jiya ma an kai hari kan kwambar motocin gwamnan Aden inda kimanin mutum 6 su ka rasa ran su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.