• Thu. Dec 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

BOM YA HALLAKA AKALLA MUTUM 35 A KASUWA A IRAKI

Wani bom da a ka dana ta hanyar kunar bakin wake ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 35 a wata kasuwa mai cunkoson jama’a a birnin Bagadaza na kasar Iraki.

An ga naman sassan jikin mutane a warwatse bayan tashin bom din yayin da mutane ke sayaiya don bukin babbar sallah.

Kazalika mutum 60 sun samu raunuka a sanadiyyar bom din.

Shugaban Iraki Barham Salih ya nuna takaicin cewa masu harin sun ki barin mutane su ma yi murnar lokacin idi, ya na mai zaiyana harin da mummunan laifi.

Akwai mata 8 da yara 7 cikin wadanda su ka rasa ran su.

Iraki ta tabbata helkwatar mutuwa tun kifar da gwamnatin marigayi Saddam Hussien a 2003.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,639 thoughts on “BOM YA HALLAKA AKALLA MUTUM 35 A KASUWA A IRAKI”
  1. What’s up, constantly i used to check website posts here early in the morning, because i like to find out more and more.