• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BIDEN YA FARA SAUYA MANUFOFIN TRUMP

Sabon shugaban Amurka Joe Biden ya fara sauya manufofin tsohon shugaban kasar Donald Trump da su ka hada da kin jinin baki da musulmi.

Tun a jawabin sa na rantsuwar hawa mulki, Biden ya ce zai zama shugaban dukkan Amurkawa ne ba tare da nuna bambancin fifikon jar fata kan farar fata ba.

Tuni shugaban ya soke takaita ba da izinin shiga kasar ga masu son yin hakan daga kasashen musulmi.

Hakanan a na sa ran Biden zai bude dama ga ‘yan ketare su samu aiyukan yi a kasar da a baya Trump ya ce hakan tamkar kwace guraben aiki ne ga ‘yan kasa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.