• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BIDEN NA DUBA YIWUWAR MAIDA SUNAN IYAN TAWAYEN HOUTHI A JERIN ‘YAN TA’ADDAN DUNIYA

ByNoblen

Jan 21, 2022

Shugaban Amurka Joe Biden na duba yiwuwar maida sunan ‘yan tawayen houthi na Yaman a jerin sunayen ‘yan ta’addan duniya a bakin littafin Amurka.
Biden na amsa tambaya ce a taron manema labaru na aiyana cikar sa shekara daya kan mulki.
Duk Biden ya fi bayani kan lamuran cikin gida, amma ya amsa tambaya kan Rasha da Ukraine da kuma batun na Yaman.
Shugaban na Amurka ya ce ya na nazari kan maida sunan houthi a jerin kungiyoyin ta’addanci.
Makwanni bayan hawan sa mulki, Biden ya cire sunan houthi daga jerin sunayen ‘yan ta’adda don sauya manufofin tsohon shugaba Donald Trump da ke daukar houthi da Iran ke marawa baya a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Kazalika Biden ya tsara dawo da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar 2015 ta dakatar da kera makaman kare dangi da Iran din ke yi.
Houthi ta kara daukar hankalin duniya biyo bayan harin da ta kai Daular Larabawa da jirgi marar matuki inda hakan ya yi sanadiyyar rasa ran mutum uku.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.