• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BAZOUM ZAI KARBI RAGAMAR MULKIN JAMHURIYAR NIJAR

A yau jumma’ar nan Bazoum Muhammad ya ke shan ruwa don karbar ragamar shugabancin jamhuriyar Nijar.

Bazoum wanda hukumar zaben kasar CENI ta aiyana a matsayin wanda ya lashe zabe a zagaye na biyu ya yi takara a karkashin jam’iyyar gwamnati PNDS taraiya inda ya yi karon batta da dan takarar adawa na jam’iyyar RDR Muhammad Ousmane.

Wannan dai ya nuna zarcewar jam’iyyar gwamnati ta shugaba mai barin gado Muhammad Issoufou da ya yi mulki wa’adi biyu na tsawon shekara goma.

‘Yan adawa na cigaba da kalubalantar sakamakon zaben duk da nasarar da kotu ta ba wa Bazoum.

Wasu ‘yan Nijar na daukar Bazoum a matsayin ba cikekken dan Nijar ba kuma mai yiwuwa ya zama mai kare muradun kasar Faransa da ta yi wa kasar mulkin msllaka maimakon damuwa da bukatun ‘yan Nijar.

Duk da haka Bazoum ya yi fatar cigaba da samun goyon baya don sauke nauyin da ya ce al’ummar Nijar sun dora ma sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *