• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BAYAN WATA 13 LEBANON TA KAFA GWAMNATI

ByNoblen

Sep 11, 2021 ,

Shugabanni a Lebanon sun amince da kafa gwamnati mai ministoci 24 bayan wata 13 ba amintacciyar gwamnati mai tasiri.

Gwamnatin dai na karkashin firaminista Najib Mikati.

Faransa ce da hadin guiwar Amurka har ma da tuntubar Iran ta sa kafa gwamnatin ta matsin lamba.

Mikati ya ce tamkar a yanzu shugabannin Lebanon sun shiga jirgi ne, don haka sai su daura damara don tunkarar matsanancin faduwar darajar kudin kasar da sam zai hana gwamnatin yin rangwame kan komai.

Mikati wanda ya zubar da hawaye gaban ‘yan jarida, ya ce gwamnatin sa za ta bukaci kasashen duniya su tallafa don samar muhimman a abubuwan masarufi da kasar ke bukata.

Kamar yanda mu ka sha bayanin tsarin siyasar Lebanon, shugaban kasar kan zama kirista, firaminista musulmi dan ahlussunnah inda shugaban majalisa kan zama dan shia.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.