• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BAUCHI DA ZAMFARA SUN YI CANJARAS A GARAMBAWUL

Daga zaben 2019 a Najeriya, za a iya cewa gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir da na Zamfara Bello Maradun sun dau mataki na garambawul din ‘yar gaba daya ga dukkan jami’an gwamnatin su.

Ba kamar yanda a ke gani a wasu jihohin yanda a kan sauya kwamishina biyu zuwa uku ko sauyawa wasu ma’aikatu ba, gwamnonin biyu sun sallami dukkan jami’an gwamnatin ne daga mulki in ka debe wasu ‘yan kalilan a Bauchi da su ka shafi labaru da tsaro.

Wasu na sharhin garambawul din na da nasaba da muradun siyasa na gwamnonin biyu don samun sabon zubin da zai taimake su tazarce a 2023.

Hakanan akwai raderadin gwamnonin biyu na PDP na sharar dagen sauya sheka zuwa APC ne.

Yanzu dai za a jira a ga gudun ruwan wadannan matakan masu ban mamaki a lokaci daya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.