• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BATUN SUNAYEN MASU DAUKAR NAUYIN BOKO HARAM

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa ba zai iya fadar sunayen masu ɗaukar nauyin ayyukan Boko Haram ba.

Ya bayyana haka ne a hira da aka yi da shi a Channels TV inda wakilin gidan talabijin ɗin ya tambayeshi cewa ga ƙasar UAE ta fallasa masu daukar nauyin ta’addanci, shin me zai hana gwamnatin Najeriya ma ta yi haka?

Bawa yace ba zai iya bayyana sunayen wanda ke ɗaukar nauyin ta’addancin ba dan kuwa abune na sirri.

Yace amma suna aiki tuƙuru tare da sauran hukumomin gwamnati da kuma ƙasashen waje dan ganin an yi maganin matsalar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *