• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BATUN HARBO JIRGIN UKRAINE DA IRAN TA YI A BARA

ByNoblen

Dec 17, 2021 ,

Hakurin kasashen da fasinjojin su, ke cikin jirgin Ukraine da Iran ta harbor a 2020 ya fara karewa, inda su ka ba wa Iran wa’adin zuwa 5 ga Janairu mai zuwa ta fara batun diyya ko su dau mataki na gaba.
Kasshen sun hada da Burtaniya, Kanada, Sweden da Ukraine.
Yawancin fasinjoin jirgin 176 da duk su ka riga mu gidan gaskiya ‘yan kasashen 4 ne.
Kasashen sun ce Iran na tafiyar hawainiya kan yin adalci ga wannan ganganci na harbe jirgin sama da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba su yi wa Iran din laifin komai ba.
Iran ta ce lalle ita ta harbor jirgin cikin kuskure don bayanan da ba daidai ne na masu tsaron sararin samaniyar ta da kuma wanda ya ke aiki a lokacin da akasin ya auku.
Kasar ta ‘yan shia ta ce a lokacin da ta harbor jirgin a na tsakiyar zullumi ne a tsakanin ta da Amurka sanadiyyar kashe babban kwamnadanta Qassim Sulaimani da Amurka ta yi a Iraki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “BATUN HARBO JIRGIN UKRAINE DA IRAN TA YI A BARA”
  1. Excellent items from you, man. I’ve take into accout your stuff prior to and you’re just too magnificent. I really like what you’ve received here, certainly like what you’re stating and the way in which during which you are saying it. You make it enjoyable and you still take care of to keep it sensible. I cant wait to read much more from you. This is actually a great site.

Leave a Reply

Your email address will not be published.