• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BATUN GWAMNA OBASEKI KAN BUGA KUDI NAIRA BILIYAN 60 DON RABAWA JIHOHI-GWAMNATIN TARAIYA

Gwamnatin Najeriya ta musanta bayanin gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da ya ce gwamnatin a watan maris ta buga kimanin naira biliyan 50-60 don cikata kudin kason wata ga jihohi.

Obaseki ya alakanta batun buga kudin ga karancin kudi da ke hannun gwamnatin taraiya da ya tilasta buga adadin da a ke bukata don rabawa jihohi.

Ministar kudi Zainab Ahmed ta zaiyana bayanin da cewa Obaseki ya yi karya ne kan wannan ikirarin.

Zainab da ta ke magana da manema labaru a fadar Aso Rock ta zaiyana kalaman Obaseki da cewa abun takaici ne.

Ministar ta ce an samu kudin da a ka raba ta hanyoyi daban-daban da a ke tara kudin shiga amma batun an buga kudi ba gaskiya ba ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *