Barayin da su ka sace shugaban karamar hukumar Keffi da direban sa a wajajen kauyen Gude a jihar na bukatar kudin fansa Naira miliyan 30.
A ranar jumma’a da magariba barayin su ka tare motar shugaban karamar hukumar Muhammad Baba Shehu yayin da ya ke dawowa daga wani taro a Lafiya.
Miyagun sun harbe jami’in ‘yan sanda da ke tsaron lafiyar shugaban karamar hukumar Sajan Alhassan inda Allah ya yi ma sa rasuwa.
Rahotanni sun baiyana cewa barayin sun bugo waya su na bukatar kudin fansa da ba da hakurin kisan gilla da su ka yi wa sajan Alhassan.
An ba da labarin cewa barayin kan fito musamman in dare ya fara a kan hanyar Keffi zuwa Akwanga a jihar Nasarawa
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀