• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BARAYIN DAJI-MAJALISAR DATTAWA NA DAUKAR MATAKAN HANA BIYAN KUDIN FANSA

Majalisar dattawan Najeriya na daukar matakan hana biyan kudin fansa daga masu satar mutane ta hanyar gyara ga dokar yaki da ta’addanci.
Kudurin gyaran dokar ya cimma karatu na uku kuma na karshe kenan don amincewa da gyaran da zai maida biyan kudin fansa ya zama haramun.
Shugaban kwamitin sashen shari’a da ‘yancin dan-adam Opeyemi Bamidele ya gabatar da kudurin da nuna manufar sa shi ne yaki da barayin daji don hana su samun kudin da zai rika zuga su, su yi ta sace mutane.
Bamidele ya kara da cewa gyaran zai sa daukar matakan hana ‘yan ta’adda amfani da tsarin bankuna waken tura kudaden da su ka samu ko kuma a turo mu su kudin.
Dama jihar Kaduna da ta fi kowacce a yanzu wajen satar mutane ta hana ba da kudin fansa ga barayin da hakan kuma kan jefa rayuwar wadanda a ka sacen a cikin hatsari.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “BARAYIN DAJI-MAJALISAR DATTAWA NA DAUKAR MATAKAN HANA BIYAN KUDIN FANSA”
  1. I am so happy to read this. This is the kind of manual that needs to be given and not the accidental misinformation that’s at the other blogs. Appreciate your sharing this greatest doc.

Leave a Reply

Your email address will not be published.