• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BARAYIN DA SU KA SACE DALIBAN ISLAMIYYA NA NEJA NA CI GABA DA TSAURARA MATSAYA

Barayin da su ka sace daliban Islamiyya na Salihu Tanko a Neja na cigaba da tsaurara matakai don neman karin kudin fansa.

Wannan na faruwa ne duk da tura Naira miliyan 30 da iyayen su ka yi da kuma barayin su ka ce kudin ba su cika ba.

Majiyoyin barayin na haddasa fargabar cewa uku daga daliban sun riga mu gidan gaskiya duk da dai ba a tantance sahihancin labarin ba.

Mai mika kudin fansar Kasimu Barangana da barayin su ka sako bayan rike shi don nuna kudi ba su cika ba, ya ce an raba yaran a bigire 25.

Daliban dai daga Tegina a karamar hukumar Rafi, sun shafe kusan wata biyu a hannun barayin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “BARAYIN DA SU KA SACE DALIBAN ISLAMIYYA NA NEJA NA CI GABA DA TSAURARA MATSAYA”
  1. Hi to all, how is the whole thing, I think every one is getting more from this web site,
    and your views are fastidious designed for new people.

Leave a Reply

Your email address will not be published.