• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BARAYI SUN YI WUF SUN SACE NAIRA MILIYAN 31 A GIDAN GWAMNATIN JIHAR KATSINA

Rahotanni daga majiyoyin jaridar PREMIUM TIMES na baiyana cewa barayi sun shiga gidan gwamnatin jihar Katsina su ka sace Naira miliyan 31.

Labarin ya nuna an shiga ofishin mai kula da kudi na gidan gwamnatin inda a ka dauke kudin kuma kamarar tsaro ta nuna hoton wani mutum daya ne na neman shiga ginin ta wata taga da rufaffiyar fuska.

Kudin dai na daure cikin wani buhu ne yayin da mai satar ko masu satar su ka dauke su.

Hakanan an baiyana cewa tuni a ka kaddamar da bincike don gano wadanda su ka aikata wannan satar na rainin wayo.

A bariya ma an samu irin wannan sata amma ta Naira miliyan 16 daga ofishin sakataren gwamnatin jihar inda a ka cafke wasu da a ke tuhuma da hannu a satar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.