• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BARAYI SUN SACE WAYOYIN MUTANE DA DAMA A RIBIBIN SHIGA EAGLE SQUARE

Barayi da musamman ‘yan yankan aljihu sun yi abun da su ka ga dama a ribibin shiga dandalin EAGLE don babban taron jam’iyyar APC.
Barayin wadanda su ka shirya don satar, kan faki jama’a wadanda ba su lura ba, su dauke mu su da ‘yan sulallan da ke aljihun su.
Mutane da dama ba su ankara da cewa an sace wayar su, sai can in sun natsu su ka lura ba a buga mu su waya sai su duba su ga babu.
Akalla an kama wasu daga barayin amma ba lalle a ce wadanda su ka rasa wayoyin su, ko kudin su, sun samu ba.
Abun tausayi wasu tsohuwar ‘yar siyasa da ta yi ta yunkurin magana da gwamna Abdullahi Umar Gnaduje, ba ta samu dam aba, don an dauka tamkar ta na da tabin hankali inda a ka wujijjiga ta a ka ture can gefe amma ta sake wuf ta dawo duk da haka a ka kange ta.
Gwamna Ganduje na zaune da mataimakin sa Nasiru Gawunna da Sanata Kabiru Gaya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “BARAYI SUN SACE WAYOYIN MUTANE DA DAMA A RIBIBIN SHIGA EAGLE SQUARE”
  1. Hey, I think your site might be having browser compatibility issues. When I look at your blog site in Opera, it looks fine but when opening in Internet Explorer, it has some overlapping. I just wanted to give you a quick heads up! Other then that, very good blog!

  2. Asking questions are actually pleasant thing if you are not understanding
    anything totally, but this article gives pleasant understanding yet.

Leave a Reply

Your email address will not be published.