• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BARAYI SUN SACE SARKIN BUNGUDU A KAN HANYAR ABUJA ZUWA KADUNA

Rahoto na baiyana cewa barayi sun sace Sarkin Bungudu a jihar Zamfara Alhaji Hassan Attahiru a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Barayin sun bude wuta kan kwambar motocin Sarkin mai daraja ta daya inda jamu’an tsaron sa su ka maida wuta amma barayin su ka ci galaba kan su inda su ka tafi da Sarkin zuwa tungar su a daji.

Wannan na faruwa a lokacin da jami’an tsaro ke kai hare-hare kan maboyar barayin a jihar Zamfara.

Ba karin bayani sosai kan wannan akasin da kuma matakan da hukumomi za su dauka don ceto basaraken.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *