• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BARAYI SUN SACE DALIBAN ISLAMIYYA

Barayi a yankin Faskari na jihar Katsina sun sace daliban makarantar Islamiyya su 9 a yayin da su ke dawowa gida daga karatu da yamma.

Barayin kan tafi a runduna yayin aikata irin wannan mugun aiki don haka ya kan zama abu mai wuya a iya ceto wadanda a ka sace nan take.

Jaridar yanar gizo da ta ruwaito rahoton, ya ce barayin ba su bugo waya don fadar abun da su ke bukata don sako yaran ba.

Yaran kanana ne daga shekaru 12 zuwa 19.

Katsina na daga jihohin da ke matukar fama da illar barayin mutane.

Hakanan an ce a na ganin yaran wani babban barawo da a ka kashe Dogo Nabajallah ne su ka sace yaran.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *