• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BARAYI NA BARAZANA GA MANOMA TA HANYAR BUYA A DAZUKA

ByYusuf Yau

Jul 9, 2021 , , ,

Alamu na nuna noma a dumanar bana zai yi wuya a yankin karamar hukumar Birnin Gwari da Chikun a jihar Kaduna don kalubalen barayin mutane.

Kananan hukumomin biyu na daga mafi tsananin samun illar barayin a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Manoma dai na fargabar shiga gonaki da dazukan bayan gari don fargabar gamuwa da barayin da kan iya fitowa satar a kowane lokaci.

Jihar Kaduna dai yanzu tamkar ta zama mafi fama da matsalar satar mutane a Najeriya.

Yanzu haka akwai dalibai makaranta kusan 120 a hannun barayin da kan nemi miliyoyin Naira a matsayin fansa kafin sake wadanda su ka kama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *