• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BANGAREN MOQTADA SADR YA YI GALABA A ZABEN MAJALISAR DOKOKIN IRAKI

ByNoblen

Dec 1, 2021

An fito da sakamakon zaben majalisar dokokin Iraki inda a ka tabbatar da bangaren Moqtada Sadr ya samu galaba kan sauran jam’iyyu da ke alakar kud da kud da Iran.
An zargi kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran da kawo yanayin hargitsa zaben don karkatar da nasara zuwa bangaren su.
Sadr wanda babban jigon ‘yan shia ne amma wanda ba ya tare da mamayar Iran, ya samu kujeru 73 cikin 329.
Jam’iyyar Fatah ta zama ta biyu da nasara ta can nesa da kujeru 17.
Fatah na tare da kungiyoyi masu samun goyon bayan Iran.
Akasarin mutan Iraki duk da tasirin shi’anci amma ba sa goyon bayan kungiyoyin ta’addancin da Iran ta dasa a kasar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.