• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BAN YARDA BA DA YANDA A KA TSARA MUKABALA BA INA SON A SAKE SABUWA-ABDULJABBAR

Shugaban kungiyar ashabul kahfi da a ka fi sani dan’yan kogo Abduljabbar Nasiru Kabara ya ce ya na bukatar a sake wata mukabalar don bai gamsu da tsarin da a ka yi ba.

Abduljabbar wanda ya ce ba a ba shi lokaci mai yawa ya yi magana ba, ya bukaci a ba shi dama ya sake shiryawa don wata mukabalar.

Ba wannan shi ne karo na farko da Abduljabbar ke daukar salon cewa sai an yi wani shiri na musamman kafin ya shiga mukabala ko ma sai an rubuta ma da tambayoyi a rubuce don ya bi su daki-daki ya amsa bayan kara bincike.

Duk tambayoyin da a ka yi sun fito karara daga kalaman Abduljabbar a wajen tarukan majalisin sa don haka kamar ba bukatar wani sabon shiri fiye da ya ba da amsa ko ya bude littafi ya nuna abubuwan da ya yi ikirari.

An ji irin wannan salo na Abduljabbar na jam kafa kan mukabalar da ya ke cewa ya a son a yi, a wata waya tsakanin sa da Dr.Rabiu Rijiyar Lemo.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *