• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BALERI YA SAKE DALIBAN GREENFIELD BAYAN KARBAR KUDIN FANSA

Madugun barayin mutane Sani Jalingo da a ka fi sani da BALERI ya sako dalibai 14 na jami’ar Greenfield bayan karbar kudin fansa daga iyayen daliban.

In za a tuna Baleri ya nemi Naira miliyan 100 da manyan babura 10 kafin sake dalibn, ya na mai cewa Naira miliyan 55 da a ka ba shi tun farko na shan gwarin kwakwin daliban ne.

Majiya ta tsbbatar da barawon ya sassauto da kudin fansar har kasa da Naira miliysn 50 da wasu baburan hawa irin wadanda ‘yan boko haram ke amfani da su a daji.

Tun farko Baleri ya jagoranci kashe 5 daga daliban don firgita iyayen yaran su miko fansa da hakan ya saba da umurnin gwamnatin Kaduna da ke cewa ba da fansar hanya ce ta karfafawa barayin guiwa su cigaba da mugun aikin su.

Gwamnatin Kaduna ta yi maraba da dawowar daliban.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.