• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABU WATA JAM’IYYA A WAJE NA MAI TASIRI BA YA GA PDP-UDOM EMMANUEL

Gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ya ce shi dai a wajen sa ba wata jam’iyya mafi karfi irin PDP kuma ita kadai ta sani.
Emmanueal na magana ne a ganawa da wata tawagar manyan ‘yan jarida a ofishin sa da ke babbar birnin jihar Uyo.
Gwamnan wanda ya ke wa’adin sa na biyu kan mulki, ya nuna tamkar bai damu da yanda wasu gwamnoni su ka sauya sheka daga PDP zuwa APC ba.
Emmanuel wanda ya ke magana a bayan sa da tutar PDP mai tambarin lema. ya ce ya na ganin jam’iyyar ta su da ke cikin kalubalen masu sauya sheka, ita ce ke da dabarun kawar da matsalolin da ke addabar Najeriya.
Duk da haka Emmanuel ya ce duk mai tunanin raba Najeriya bai san abun da ya ke yi ba don hakan tamkar fadawa maliya ne da yasa.
In za a tuna tsohon gwamnan jihar Godswill Akpabio ya samu sabani da Emmanuel har ya so hana shi tazarce a zaben 2019.
Akpabio ya koma APC ya yi tallata jam’iyyar a jihar amma bai samu nasara ba sai dai ya samu sa’a shugaba Buhari ya nada shi babban ministan Neja Delta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “BABU WATA JAM’IYYA A WAJE NA MAI TASIRI BA YA GA PDP-UDOM EMMANUEL”
  1. If some one wishes to be updated with newest technologies therefore he must be pay a visit this web site and be
    up to date everyday.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *