• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAR KOTUN TARAIYA TA YI WATSI DA BUKATAR EMEFIELE TA BA SHI HURUMIN TAKARA

Babbar kotun taraiyar Najeriya a Abuja ta yi watsi da bukatar gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele da ke son kotu ta tabbatar ma sa hurumin yin takarar shugabancin Najeriya.
Gabanin karar an yi ta samun masu sukar yanda za a ce gwamnan babban banki ya fada siyasar yin takara irin ta shugaban kasa.
Hakanan Emefiele na bukatar yin takarar alhali ya na kan gadon aikin san na shugaban babban bankin Najeriya da kula da tattalin arziki .
Babban lauya Mike Ezekhome ya ce ba wata doka da ta hana Emefiele yin takara don haka ya na shiga siyasa ne cikin hurumin da ya ke da shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.