• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAR KOTUN TARAIYA TA WANKE ANDREW YAKUBU KAN ZARGIN BADAKALAR DALA MILIYAN 9.8

Babbar kotrun taraiya ta wanke tsohon shugaban kamfanin NNPC Mr. Andrew Yakubu bisa zargin badakalar dala miliyan 9.8.
Tun a 2017, hukumar yaki da cin EFCC ta kai samame wani gidan Yakubun da ke Sabon Tasha a Kaduna inda ta jide kudin.
Daga nan EFCC ta shigar da karar cewa Yakubu ya samu kudin ne ta hanyar da ba ta dace ba kuma kudin ba su bi ta banki ba.
Andrew Yakubu ya shaidawa kotu cewa kudin sun taru ne daga kyaututtukan da ya samu daga abokan sa bayan ajiye aiki a 2014.
Yakubu ya ce ya tara kudin ne a waje daya da kadan-kadan ba wai a dunkule ya same su ba.
Mai shari’a Ahmed Muhammed ya yanke hukuncin wanke Yakubu da umurnin a mayar ma sa kudin sa don kotu ta gamsu da hujjojin da Yakubu ya gabatar.
Kotun ta ce EFCC ta gaza bincika gaskiyar an tara kudin ne da kadan-kadan kuma ba ta taba kawo kudin gaban kotun ba tun fara shari’ar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.