• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAR KOTUN TARAIYA A ABUJA ZA TA YANKE HUKUNCI KAN FAISAL MAINA

Babbar kotun taraiya ta Abuja za ta yanke hukunci kan shari’ar dan tsohon shugaban kwamitin aiki da cikawa na fansho Abdulrashida Maina wato Faisal.

Alkalin kotun Okon Abang zai yanke shari’ar a ranar 2 ga watan Oktoba.

A na zargin Faisal da boye wasu kudi daga tuhumar wawure kudi da mahaifin sa ya yi lokacin ya na jagorantar kwamitin fansho.

Matashi Faisal Maina ya arce daga Najeriya a bara inda ya nufi Amurka kasancewar ya na da takardar kadancewa Ba’Amurke.

Mahaifin faisal, Abdulrashid Maina wanda a ka iza keyar sa daga Nijar a ka dawo da shi Najeriya bayan saba ka’idar beli, na cigaba da zaman shari’ar tuhumar sa da almundahanar Naira biliyan 2.1.

Da alamu Jostis Abang zai yanke hukunci a bayan idon Faisal bayan da hukumar yaki da cin hanci EFCC ta kammala tattara hujjojim ta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *