Babbar alkalin jihar Akwa Ibom Ekaete Obot ta gwale wani lauya wanda ya zo kotu ya na cewa kotun ta saba tsarin mulki a hukuncin da ta gabatar bara.
Lauyan Inibehe Effiong na magana ne kan shari’ar da kotun ta yanke inda ta ba wa gwamnan jihar Udom Emmanuel diyyar naira biliyan 1.5 don yi ma sa kage.
Effiong ya dage sai kotun ta saurari bayanin amma hakan har ya kai ga lauyan sashen shigar da kara Samuel Ikpo ya ma sa tsawa cewa ya zauna.
Mai shari’a Obot ta bukaci lauyan ya rufa ma ta baki don ba a shirin talabijin na channels ya ke magana ba ya na gaban kotu ne.
Hakanan Obot ta ce Effiong ba zai koya ma ta aikin ta ba da ta share fiye da shekaru 30 ta na yi.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀