• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAN SUFETON ‘YAN SANDAN NAJERIYA YA YI WATSI DA RA’AYIN BASHI DA KATABUS A RUNDUNAR

Babbban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu ya yi watsi da wata hira da a ka yi da wani jami’in soja mai ritaya Manjo Janar Garba Wahab wanda ya ce ba sufeton ne ke jagorantar rundunar ‘yan sandan ba ko kuma a ce ba shi da katabus a kan jagorancin rundunar.

Wahab wanda gidan talabijin na Channels ya zanta da shi, ya ce babban sufeto ya zauna kan kujera da duk Mayan aikin tsaro amma abun da ya gagare shi, shi ne rundunar ba ta karkashin jagorancin sa.

A sanarwa daga kakakin rundunar Frank Mba, babban sufeton ya ce shi ke rike da jagorancin rundunar kam-kam.

Sanarwar ta ce Wahab ya yi magana ne da jahiltar yanda lamura ke tafiya a karkashin tsarin dimokradiyya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “BABBAN SUFETON ‘YAN SANDAN NAJERIYA YA YI WATSI DA RA’AYIN BASHI DA KATABUS A RUNDUNAR”
  1. Heya i am for the first time here. I came across this board and
    I find It really useful & it helped me out much. I hope to give something
    back and help others like you helped me.

  2. I know this web page provides quality depending content and
    additional material, is there any other web page which gives these kinds of information in quality?

Leave a Reply

Your email address will not be published.