• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAN SUFETON ‘YAN SANDAN NAJERIYA YA TAKAITA ZIRGA-ZIRGAR MOTOCI A JIHAR EDO DAGA DARE ZUWA YAMMACIN ASABAR DIN NAN

ByNoblen

Sep 19, 2020 , , ,

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya ba da umurnin takaita zirga-zirgar motoci a jihar Edo daga dare zuwa yammacin asabar din nan don gudanar da zaben gwamnan jihar. Dokar za ta daina aiki ne daga karfe  6 na yammacin asabar din bayan kammala tattara sakamakon zabe daga rumfuna zuwa cibiyoyin tara sakamakon. Sanarwa daga rundunar ‘yan sandan ta ce matakin takaita zirga-zirgar don hana jigilar ‘yan bangar siyasa ne da ka iya wargaza zaman lafiyar zaben hakanan da hana wasu miyagu daga ketowa cikin jihar daga jihohin makwabta. Dubban ‘yan sanda ne su ka shiga jihar Edo don kula da gudanar da zaben.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “BABBAN SUFETON ‘YAN SANDAN NAJERIYA YA TAKAITA ZIRGA-ZIRGAR MOTOCI A JIHAR EDO DAGA DARE ZUWA YAMMACIN ASABAR DIN NAN”
  1. For the reason that the admin of this web page is working, no hesitation very quickly it will be famous,
    due to its quality contents.

  2. If you are going for best contents like I do, just go to see this web page daily since it provides quality contents, thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published.