• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAN SUFETON ‘YAN SANDA YA SAUYA KWAMISHINAN SA NA ANAMBRA DON INGANTA YAKI DA ‘YAN AWARE

Mukaddashin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali ya sauya kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra Moday Bala Kuryas inda ya nada Christopher A.Owolabi ya maye gurbin sa.

Sanarwa daga kakakin ‘yan sanda Frank Mba na nuna wannan daya ne daga matakan da rundunar ke dauka don inganata tsaro a yankin kudu maso gabar da kudu maso kudu inda a ke kai hari kan jami’an tsaro da ma fararen hula ‘yan arewa daga masu rajin kafa kasar Biafra.

An tura Monday Kuryas Lagos don kula da sashen yaki da zarmiya na rundunar ‘yan sandan.
Yanzu dai za a iya cewa yankin kudancin Najeriya ya zama mai barazana ga rayukan wasu sashen jama’a inda a ke danganta hakan na neman tada fitina ko ma yaki da kuma ‘yan siyasa masu nazartar makomar su a babban zaben Najeriya a 2023.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.