• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAN SHAGON NEXT A ABUJA YA KONE KURMUS

ByNoblen

Dec 27, 2021 ,

Babban shagon sayar da kayan masarufi NEXT CASH N CARRY da ke Abuja ya kama da wuta inda yak one kurmus.
Wutar ta fara da misalign karfe 8 na safiyar lahadi inda ta samar da wani gagarumin bakin hayaki da za a iya hangowa daga nesa.
Jami鈥檃n kashe gobara daga sassa daban-daban na Abuja sun garzaya bigiren da kan titin Ahmadu Bello a yankin Jahi kan sabuwar hanyar Gwarinpa.
An ba da labarin wasu masu son na bulus sun yi ta kokarin satar kaya daga shagon da ba mamaki sun dauka wata ganima ce.
Daidai wannan lokaci na karshen shekara shagon a makare ya ke da kaya don haka asarar za ta iya zama da girman gaske.
Zuwa rubuta wannan labara ba a samu dalilin aukuwar gobarar ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI馃榾馃榾馃榾
One thought on “BABBAN SHAGON NEXT A ABUJA YA KONE KURMUS”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *