• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

Babban kuskuren da ‘yan Najeriya za su tafka shine su zabi PDP a 2023, jigon APC

ByAuwal Ahmad Shaago

Nov 29, 2021

Wani jigo a jam’iyyar APC ya bayyana abubuwan da yake gujewa ‘yan Najeriya idan suka zabi PDP a 2023 Jigon ya bayyana cewa, babban kuskure ne ‘yan Najeriya su sake amincewa da PDP ta kara mulkarsu a nan gaba Ya bayyana irin barnar da jam’iyyar PDP tayi a tsawon shekaru 16 na mulkinta, inda yace su suka bata kasar nan.

 

 

Darakta Janar na Voice of Nigeria, Osita Okechukwu, ya ce ‘yan Najeriya za su tafka babban kuskure ta hanyar mayar da jam’iyyar adawa ta PDP mulki a 2023.

 

 

Ya bayyana cewa PDP ba abar yarda bace don ceto Najeriya saboda masu tallata jam’iyyar suna da sha’awar cin hanci da rashawa da ba za ta iya warkewa ba da kuma tarihin rashin iya tafiyar da tattalin arziki.

 

 

Ya na mai da martani ne kan shirin ceto kasa da jam’iyyar PDP ta ce ta yi ne domin kawar da Najeriya daga matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da ta ce gwamnatin APC ta jefa al’ummar kasar a ciki.

 

 

 

Punch ta ruwaito shi yana cewa:

 

“Ta yaya ‘yan Najeriya za su amince da ‘yar uwar jam’iyyar PDP, ganin cewa magabatanta na cike da gibin amana? Mun san cewa abubuwa na da wuya; Ina ganin gara a bar APC ta gyara Najeriya. Daga ina ake farawa?”

 

 

Okechukwu wanda jigo ne a jam’iyyar APC reshen jihar Enugu, ya bayyana cewa har yanzu Najeriya ba ta gama farfadowa daga cin zarafi da cin hanci da rashawa da PDP ta jefa kasar a tsawon mulkin ta na shekaru 16.

 

 

 

Okechukwu ya kuma kara da cewa hukumar EFCC na ci gaba da bincike kan zargin damfarar miliyoyin Naira da wani dan jam’iyyar Kassim Afegbua ya yi kan shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da aka tsige.

 

 

 

Ya kuma yi nuni da cewa ‘yan Najeriya ba za su manta da badakalar kudade daban-daban da suka hada da zamba ta Halliburton har zuwa badakalar Dasuki ba.

 

 

Okechukwu ya kuma yi tambaya cewa:

 

 

“Shin za mu iya mantawa da almubazzaranci da aka yi wa matatun mai na Greenfield na Dala biliyan 23 – daya a Legas, daya a Kogi daya kuma a Bayelsa?

 

 

 

Hakazalika, ya ci gaba da kawo misalai da suke da alaka da cin hanci da rashawa daga mambobi da jiga-jigan jam’iyyar PDP da ta yi mulki a baya.

 

 

 

Sai dai, lokuta da dama Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a 2019 yakan ce shi ne zai iya gyara Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

 

 

 

 

 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “Babban kuskuren da ‘yan Najeriya za su tafka shine su zabi PDP a 2023, jigon APC”

Leave a Reply

Your email address will not be published.