Babban hafsan rundunar sojan kasan Najeriya laftanar janar Ibrahim Dahiru ya rasa ran sa a sanadiyyar hatsarin jirgin sama.
Akasin ya auku ne a tsakanin Abuja da Kaduna inda jirgin na soja ya fadi kuma ya kama da wuta.
Attahiru na tare da sashen mataimakan sa a jirgin wadanda su ma su ka rasa ran su.
Marigayin wanda ya karbi aiki bayan murabus din tsohon hafsa Tukur Buratai, ya yi alwashin aiki tukuru don magance kalubalen tsaro.
A wani faifan bidiyo an ga babban hafsan na karfafawa dakaru guiwa ta hanyar kalmomin kirari irin na soja don tunkarar ‘yan ta’addan Boko Haram.
Cikin manyan jami’ai da hatsarin jirgin sama na soja ko mai saukar angulu ya yi sanadiyyar rayuwar su, sun hada da tsohon mai ba da shawara kan tsaro Andrew Azazi, tsohon gwamnan soja na Kano Abdullahi Wase, tsohon mukaddashin babban sufeton ‘yan sanda John Haruna da sauran su.