• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAN BANKIN NAJERIYA YA DAKATAR DA YI WA SABBIN KAMFANONIN CANJI LASISI

Babban bankin Najeriya ya dakatar da yi wa sabbin kamfanonin canji rejista a cikin matakan rage tasirin ‘yan canjin.

Wannan ya biyo bayan mataki ne da bankin ya dauka na daina ba wa ‘yan canji kudin ketare da tura kudin kai tsaye bankunan kasuwanci don samun kudin su rika yawa a cikin jama’a.

Babban bankin CBN a takaice ya ce fiye da kamfanoni 700 ke neman lasisi duk wata alhaki yanzu haka akwai sama da kamfanonin canji 5000.

‘Yan kasuwar canjin sun ce sun zuba ido don nazartar lamuran amma ba za su ce komai ba tukun.

Tuni dalar Amyrka ta haura Naira 500.

Wata majiya na nuna akwai karancin dala ne a bankin da ba zai iya biyan bukatun kasuwar canjin ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.