• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABBAN BANKIN NAJERIYA YA DAKATAR DA SAYAR DA KUDIN KETARE

Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da daukar matakin dakatar da sayarwa ‘yan kasuwar canji kudin ketare da su ka hada da dalar Amurka.

Gwamnan bankin Godwin Emefiele ya baiyana haka a zantawar kafar talabijin.

Emefiele ya zargi ‘yan kasuwar canjin da cewa su na bari a na amfani da su wajen zamba cikin aminci ta hanyar almundahanar kudi.

Gwamnan ya ce akwai hannun wasu hukumomin duniya da ma wasu ofisoshin jakadanci a wannan lamari.

Yanzu dai bankin zai rika tura kudi kai tsaye ga bankunan ‘yan kasuwa don kowa ya tafi can ya rika bin ka’ida.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.