• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BABACHIR DAVID YA JAGORANCI TAWAGAR MAIDA FOM DIN TAKARAR TINUBU BAYAN CIKEWA

Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babachir David Lawan ya jagoranci tawagar mutanen da ta mayar da fom din tsayawa takarar shugaban kasa a inuwar APC na uban jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu bayan cike bayanan da a ke bukata.

Babachir David wanda a ka kwabe daga mukamin sa bisa sakamakon binciken badakalar kudi, ya nuna kwarin guiwar Tinubu zai samu nasara.

Lawan ya kara da cewa in an duba yawan magoya baya su na kan nasara amma idan ba su samu nasara ba za su koma gida su rungumi kaddara da mara baya ga wanda ya yi nasara.

Zuwa jumma’ar nan APC za ta kulle karbar dukkan takardun tsayawa takara don shiga aikin tanatncewa a gobe asabar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.