• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA ZUWA AIKIN HAJJIN BANA KAMAR BARA

ByYusuf Yau

Jun 13, 2021 , , , ,

Bana ma ta tabbata ba damar zuwa Saudiyya don gudanar da aikin hajji kamar yanda lamarin ya faru a bara.

Hukumomin Saudiyya sun baiyana dalilin cigaba da kare rayukan jama’a daga cutar korona bairos ya jawo daukar matakin.

Yanzu mutum dubu 60 ne za su gudanar da aikin hajjin daga cikin Saudiyya kadai da su ka hada da ‘yan kasa da mazauna kasar.

Za a iya cewa an samu kari a kan bara inda mutum dubu daya ne kacal su ka gudanar da aikin hajjin cikin tsauraran matakai.

Saudiyya ta ce ta dau matakin bayan tuntubar kasashen duniya da su ka nuna ma ta fahimta kan hukuncin.

Tun gabanin nan, kasar Indunusiya da ta fi yawan alhazai a duniya ta dakatar da zuwa hajjin na bana.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.