• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA ZAN SA BAKI DON SAKE NNAMDI KANUBA-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai sa baki don sake shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu ba.
Shugaban na magana ne a zantawa da gidan talabijin na Channels da a ka saka ranar laraba.
Shugaban ya ce sashe daya da ba zai iya saka baki ba a kasar shi ne na shari’a don haka Nnamdi Kanu ya tsaya don kare kan sa a kotu.
Shugaba Buhari ya ce ba zai yiwu a bar Kanu ya na cin mutuncin Najeriya daga can kasashen turai ba don haka ya bi shari’ar da a ke yi ma sa a kotu.
Yanzu haka Kanu na hannun jami’an tsaron DSS inda mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun taraiya ke jagorantar shari’ar sa.
A na tuhumar Kanu da cin amanar kasa da laifukan ta’addanci

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *