• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA ZA MU MARAWA GAMAIYAR KUNGIYAR KWADAGO BAYA WAJEN YAJIN AIKI BA-DILLALAN FETUR

ByYusuf Yau

Sep 27, 2020 , ,

Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya “IPMAN” ta ce ba za ta shiga yajin aikin da gamaiyar kungiyar kwadago NLC/TUC  su ka shirya farawa ranar litinin din nan 28 ga watan nan na satumba.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN ya ruwaito kakakin kungiyar Yakubu Suleiman na cewa ‘ya’yan kungiyar su cigaba da gudanar da lamuran su kar su biyewa yajin aikin.

Suleiman ya kara da cewa jan tallafi na da matukar amfani ga kasa don bunkasa arzikin ta don haka IPMAN na fatar ‘yan kwadago za su ga muhimmancin janye tallafin.

A na su bangare gamaiyar kungiyar kwadago ta kammala dukkan shirye-shiryen aukawa yajin aiki don matsawa gwamnati lamba ta janye Kara farashin fetur da wutar lantarki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “BA ZA MU MARAWA GAMAIYAR KUNGIYAR KWADAGO BAYA WAJEN YAJIN AIKI BA-DILLALAN FETUR”
  1. It’s nearly impossible to find well-informed people for this subject, but
    you sound like you know what you’re talking about! Thanks

  2. Great beat ! I wish to apprentice even as you amend
    your site, how can i subscribe for a blog website?

    The account helped me a acceptable deal. I had been a little bit acquainted of this your broadcast offered brilliant transparent concept

Leave a Reply

Your email address will not be published.