• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA ZA MU IYA DAWO DA TALLAFIN MAN FETUR BA-GWAMNATIN NAJERIYA

Gwamnatin Najeriya ta ce ba zai zama alheri ba ta yi tunanin dawo da tallafin man fetur bayan janye tallafin gaba daya. Janye tallafin ya cilla farashin litar mai mafi tsada a duk tarihin kasar ta hanyar barin ‘yan kasuwa su tsaida farashin da zai sa su samu riba. Ministar kudi Zainab Shamsuna ta baiyana cewa raguwar samun kudin shiga ya sanya shugaban Buhari daukar matakin janye tallafin. Shamsuna ta ce matukar a ka dawo da tallafin zai kai ga gwamnati ba za ta iya biyan ‘yan kasuwar fetur kudi ba, sai a samu takaddama da za ta haddasa matsala. Ministar ta ce ko da farashin gangar danyen mai zai dawo irin can baya, gwamnatin ba za ta iya sake dawo da tallafin ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “BA ZA MU IYA DAWO DA TALLAFIN MAN FETUR BA-GWAMNATIN NAJERIYA”
  1. Thanks a bunch for sharing this with all of us you really recognize what you are speaking about!
    Bookmarked. Please additionally consult with my web site =).
    We can have a hyperlink change contract among us

Leave a Reply

Your email address will not be published.