• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA ZA MU CIGABA DA DAUKAR NAUYIN FOM DIN ‘YAN TAKARA BA-SULE LAMIDO

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce saboda dalilan korafin ‘yan siyasa, ba zai cigaba da jagorantar sayawa ‘yan takara kudin fom din tsayawa zabe ba, a inuwar PDP a jihar Jigawa.

Lamido a zantawa da gidan rediyon Freedom Dutse, ya na amsa tambaya ne kan shirin PDP na shiga zaben kananan hukumomi na jihar da ke karkashin jam’iyyar APC.

Sule Lamido wanda babban jigo ne a PDP a taraiya  ya ce a shekarun baya jam’iyya ke daukar nauyin fom din ‘yan takara amma sai lamarin ya jawo korafi,  wasu na cewa a na dauki dora har wanda ya yi wa jam’iyyar takarar gwamna Aminu Ringim ya nuna tamkar ba a son sa ne.

Bisa wannan dalili Alhaji Lamido ya ce an dakatar da wannan daukar nauyi don haka kowa ya sayi fom da kan sa ya gwada farin jinin sa a takarar.

Tsohon gwamnan ya ce tuni ya gano hatta a Mazabar sa a Bamaina dan takara ya kasa sayen fom din.

Wani matashi dan gane kashenin dan takarar gwamna na PDP Aminu Ringim, wato Haruna Shu’aibu Danzomo ya ce sam Lamido ba ya biyawa ‘yan takara fom kuma ko bai sa baki ba ‘yan PPD za su yi tasiri.

Danzomo ya ce tsoma bakin Sule Lamido ne ma kan jefa jam’iyyar a turbar faduwa zabe don yanda ya ke ragarwa APC da sunan a zauna lafiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.