Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ba za ta ba da dama wasu su zarge ta da neman wa’adi na uku kan mulki ba.
Shugaban na magana ne lokacin da shugaban hukumar zabe INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya ke mika ma sa rahoton hare-hare da ‘yan awaren Biafra su ka kai kan ofisoshin hukumar a kudancin Najeriya.
Don haka shugaban ya ce zai dau matakin maganin miyagun don kar ya kai ga zargin gwamnatin sa za ta nemi tazarce karo na uku bayan kammala wa’adin a 2023.
A jawabin shugaban ya ce miyagun irin sun yi cin zarafi na iya kudin su amma yanzu lokaci ya yi da za su dandana kudar su.
Kalaman shugaban sun kawo farin ciki ga masoyan Najeriya da ke fatar za a murkushe masu cin amanar kasa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀