• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA ZA A TABA AMINCEWA A KAFA KASAR BIAFRA-TSOHON BABBAN JAMI’IN AD

Tsohon babban jami’in jam’iyyar AD Alhaji Abdullahi Garba ya ce ba ta yanda za a yi a bar masu rajin kafa Biafra su kafa kasa.

A zantawar sa da manema labaru a Abuja, Alhaji Garba ya ce ba zai yi wu a bar wasu tsiraru marar sa tarbiya su raba Najeriya ba.

Dan siyasar ya ce ai masu batun a raba kasar ba da gaske su ke yi ba don kuwa ba a taba kawo batun gaban majalisar dokokin Najeriya ba.

Garba ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dau duk matakai bisa doka na cafke masu tada kaya baya da gurfanar da su gaban kotu don fuskantar shari’ar kisan gilla ko ma cin amanar kasa.

Yayin da ya ke nuna yankin arewa na cike da arziki da zai iya rike kan sa ko kaddara ta faru an samu rabuwar, ya ce a tarihi da kudin gyada da auduga a ka tono man fetur da kudu ke tinkaho da shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *