Karamin ministan fetur na Najeriya Timipre Sylva ya ce ba za a samu karin farashin litar fetur ba a watan gobe na yuni.
Tabbacin zai iya rage zullumin yiwuwar mafi girman karin farashin litar da zai iya kai wa Naira 385 bisa shawarar kungiyar gwamnoni.
Karin zai zo ne da zarar gwamnati ta janye tallafin da ta ke bayarwa don tsaida litar a yanda ta ke da tsada a halin yanzu.
In ba don babban daraktan kamfanin fetur NNPC Mele Kolo Kyari ya bada tabbacin a na ba da biliyoyin Naira a tallafi ba; tsarin gwamnatin APC ta Buhari na daukar tallafin a matsayin hanyar satar kudin al’umma.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀