• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

BA WANI SAUYIN SHUGABANCI DA A KA SAMU A APC-SAKATARE AKPANUDOEDEHE

Sakataren kwamitin rikwan APC John Akpanudoedehe ya ce sam ba wani sauyin shugabanci da a ka samu a jam’iyyar biyo bayan dambarwar da ta hargitse tsakanin gwamna Nasir Elrufai da masu mara baya ga tsohon kwamitin.
Akpanudoedehe wanda ya shigo sakatariyar jam’iyyar bayan zamudawa na wani lokaci bayan an ba da labarin ya yi murabus, ya ce gwamna Mai Mala Buni na nan kan kujerar sa kuma zai shigo ya cigaba da aikin shirya babban taro.
John Akpanudoedehe ya kara da cewa ba wani batun karbe ragama da gwamnan Neja Sani Bello ya yi kuma jam’iyyar na dagewa don ture wani umurnin kotu da ke dakatar da babban taron jam’iyyar ranar 26 ga watan nan.
Yanzu dai gwamnonin APC sun rabe gida biyu tsakanin masu mara baya ga kwamitin Buni da masu ra’ayi akasin hakan.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *